in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhangye dake kokarin kafa sansanonin shuka kayayyakin noma
2016-01-14 15:59:55 cri

Birnin Zhangye na mai da hankali matuka wajen raya aikin shuke-shuken kayan lambu domin nuna goyon bayansa ga shirin da kasar ta bullo da shi na zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21. Haka kuma, birnin ya bullo da wani shirin bunkasa kayan lambu a birnin Zhangye bisa shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na karni 21. Ya zuwa shekarar 2020, birnin na fatan zama cibiyar fidda kayan lambu na lokacin zafi a duk fadin kasar, da kuma cibiyar samar da kayan lambu a lokacin sanyi da bazara ga yankin arewa maso yammacin kasar, da kuma cibiyar shuka nau'o'in laimar kwado ta yammacin kasar Sin.

Haka kuma, ya zuwa shekarar 2020, za a kara fadin gonakin kayan lambu daga eka dubu 730 tun a shekarar 2014 zuwa eka miliyan 1, kana, kashi 70 bisa dari daga cikinsu za a shuka kayan lambu na lokacin zafi, da kuma kashi 20 bisa dari na kayan lambu, sa'an nan za a shuka kashi 10 bisa dari na nau'o'in laimar kwado, kuma bisa hasashen da aka yi, ya zuwa lokacin, za a iya samar da kayan lambun da suka kai ton miliyan 4 a ko wace shekara, kuma gaba daya darajarsu za ta kai kudin Sin RMB biliyan 8.

Da yake tsokaci kan wannan batu, shugaban sashen raya aikin amfanin gona domin samun kudin shiga na hukumar ayyukan gona na birnin Zhangye Zhang Wenbin ya yi bayani cewa,

"Mun zayyana manufar neman bunkasuwa kan wannan aiki, ciki hada da fitar da kayan lambu na loakcin zafi watau kayan lambun da ake nomawa a watan Yuni da Yuli zuwa yankin gabashin kasar, watau zuwa biranen dake kusa da teku, ciki hada da HongKong, Macao da kuma kasashen Singapore da Japan, a bangaren yammaci kuma, za mu fitar da kayan lambunmu zuwa kasashen yankin tsakiyar Asiya, da wasu kasashen dake kan hanyar siliki. "

Bugu da kari, Zhang Wenbin ya bayyana cewa, a halin yanzu, an fara amfani da tsarin sayar da kayan lambu a birnin Zhangye, ta hanyar hadin gwiwar kamfanonin sayar da hajoji zuwa ketare, kamfanonin wurin, kungiyoyin hadin kan manoman birnin da kuma kanannan manoma na birnin. A watan Mayu na shekarar 2015 kuma, kamfanin amfanin gona na birnin Zhangye ya zuba jari na kudin Sin RMB miliyan dari 3 ga yankin raya tattalin arzikin Khorgas dake yankin iyakar dake tsakanin jihar Xinjiang na kasar Sin da kasar Kazakhstan, inda ya kafa wata cibiyar sufuri, yadda za a sarrafa kayan lambu kimanin ton dubu 50 ta yadda ba za su lalace ba, ta yadda za a iya ciyar da aikin gaba a duk lardin Gansu, har ma da yankunan dake gabashin hanyar siliki.

Haka kuma, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin noma ta birnin Zhangye Wang Yong ya bayyana cewa, bisa tsarin kasar Sin da na lardin Gansu dangane da aiwatar da shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, akwai kyakkyawar makoma kan ayyukan gona na birnin Zhangye, cikin shekaru biyar masu zuwa, za a sami babban ci gaba a yankunan dake kewayen hanyar siliki a fannonin sufuri da kayayyakin more rayuwa da dai sauransu, haka kuma, matsayinmu zai ci gaba a fannin sufuri da kuma sarrafa kayayyaki da dai sauransu. Lamarin da zai taimaka matuka wajen fitar da kayayyakin gona na birnin Zhangye zuwa ketare.

"Sakamkon goyon bayan da muka samu daga kasuwanni, babu shakka amfanin gonanmu zai sami babban ci gaba saboda da yawa da kuma ingancinsu, haka kuma, a saboda manufarmu ta fuskar fitar da amfanin gona zuwa ketare, ayyukan gona da abin ya shafa za su ci gaba da bunkasa yadda ya kamata. Don gane haka, aka fito da wani shirin dake kunshe da matakai hudu, na farko a habaka gonakin masara mai fadin eka miliyan daya, na biyu, a kafa gonakin kayan lambu mai girman eka miliyan daya, na uku, a kafa sansanin kiwon shanu mai girman eka miliyan daya, na hudu, a kafa wata cibiyar shuka harawar ciyayi mai girman eka miliyan daya domin kiwon shanu. Daga bisani kuma, bisa shirin nan na zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, za a fi mai da hankali kan ayyukan shuka kayan lambu, musamman ma kayan lambu na lokacin zafi da kuma kiwon shanu, domin akwai makoma mai haske ta fuskar fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin kasashen ketare dake kewayen hanyar siliki."(Maryam)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China