160114-jinzhangye-Maryam.m4a
|
A ran 17 ga watan Nuwamba na shekarar 2014, kamfanin dake sayar da kayayyakin noma na birnin Zhangye da ke yankin tsakiya ta lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin ya sayar da kayayyakin lambu kimanin ton 83 da suka hada da nau'o'in barkono, albasa da tuffa da dai sauransu a kasar Khazakstan, ta tashar jigilar kayayyaki ta Khorgas dake jihar Xinjiang ta kasar Sin.
Wannan shi ne karo na farko da kamfanin kayayyakin noma na birnin Zhangye, har ma na lardin Gansu ya fitar da kayayyakin noma masu dimbin yawa zuwa kasashen dake tsakiyar Asiya kai tsaye. Ya zuwa karshen watan Mayu na shekarar 2015, gaba daya birnin Zhangye ya fitar da kayayyakin noma da suka hada da kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa har sama da ton dubu 70 zuwa kasashen yankin tsakiyar Asiya kai tsaye, wannan ya sa birnin ya sami kudin shiga har sama da RMB miliyan 150.
A shekarun baya, a kan sayar da galibin kayayyakin noma masu inganci da birnin Zhangye ya samar zuwa wasu biranen dake cikin kasar ta Sin, da kuma yankunan dake kudu maso gabashin kasar wadanda suke kusa da teku, sai dai ana sayar da kadan daga cikinsu a kasashen da ke yankin tsakiyar Asiya amma ba kai tsaye ba. Kana, tun bayan da aka bullo da shirin nan na zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, birnin Zhangye ya sami damar sayar da kayayyakin noman sa masu inganci zuwa kasuwannin da ke yankin tsakiyar Asiya.
Dangane da lamarin, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin noma ta birnin Zhangye Wang Yong ya bayyana cewa,
"Birnin Zhangye ya yi amfani da filaye masu girma wajen shuka kayayyakin lambu, lamarin da ya haifar da yanani mai kyau matuka dake dacewa da girman kayayyakin noma masu inganci. A halin yanzu, ana sayar da kayayyakin lambunmu a kasashen yankin tsakiyar Asiya da kuma wasu biranen kudancin kasar Sin da suka hada da GuangZhou, Shenzhen da dai sauransu. Daga bisani kuma, birnin ya fara mai da hankali sosai wajen noma kayan lambu, sakamakon bullo da shirin nan na zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, haka kuma, bisa kokarin da aka yi a wannan fanni, yanzu haka akwai gonakin kayan lambu da suka kai girman hectare dubu dari 7 a birnin, kuma ana shirin habaka shi zuwa hectare miliyan 1, domin cimma burinmu na fitar da kayayyakin mu zuwa kasashen da ke yankin tsakiyar Asiya."