in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhangye dake kokarin kafa sansanonin shuka kayayyakin noma
2016-01-14 15:59:55 cri

Birnin Zhangye dake arewa maso yammacin kasar ta Sin,yana kan tsauni ne, kuma ya dogara da ruwan da yake samu daga babban dutsen Qilian, ana iya cewa, birnin wani dausayi ne dake gabashin hanyar siliki, sabo da hamadar da kewaye birnin.

Sabo da hasken rana da ake da shi a birnin, da kuma babban yanayin zafi da sanyi a safe da dare a birnin, da rashin kwari masu barnata amfanin gona, ya taimaka wajen fitar da dimbin kayayyakin lambu masu inganci matuka daga birnin na Zhangye. Hakan ya sa, ba kawai Zhangye ya kasance sansanin fitar da hajojin amfanin gona da shuka masara na kasar ta Sin ba, haka kuma ya shahara matuka wajen fitar da kayayyakin lambu, 'ya'yan itatuwa da kuma furanni da dai sauransu, lamarin da ya sa ake kiran garin da sunan "Zhangye mai zinari".

A shekarar 2014, fadin ganakin da aka shuka kayan lambu a birnin Zhangye ya kai eka dubu 730, inda aka fitar da kayayyakin lambu iri iri har ton miliyan 2.58, gaba daya darajarsu ta kai kudin Sin RMB biliyan 2.8, kana kudin shigar manoma ya karu da kimanin kashi 15 bisa dari.

Dangane hakan, mataimakin shugaban kwalejin nazarin ayyukan gona na birnin Zhangye Wang Haohan ya bayyana cewa, aikin gona na birnin Zhangye yana kasance mai muhimmanci ga shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21. Ya ce,

"Allah ya albarkaci garin Zhangye da iska da kuma ruwa mai tsabta, har ma da kasar noma mai dausayi, abubuwan da suka taimaka mana matuka kyau fitar da amfanin gona mai tsabta. A halin yanzu, irin masara da ake nomawa a garin Zhangye ya yi suna a duk fadin kasar Sin, sa'an nan za mu ci gaba da inganta ayyukan da suka shafi kayan lambun da ake nomawa a lokacin zafi, yanzu haka an fara sayar da irin wannan kayan lambu a kasashen ketare sabo da ingancinsu, a nan gaba kuma, za a ci gaba da kyautata wannan aiki na shuka da kuma na fitar da amfanin gona mai tsabta zuwa ketare."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China