in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin ruwa dauke da bakin haure ya sake kifewa a tekun da ke dab da Italiya
2013-10-12 15:51:16 cri

Bisa labarin da muka samu daga kamfanin dillancin labaru na kasar Italiya ANSA, ya ce, wani jirgin ruwa da ke dauke da mutane kusan 250 ya kife a tekun da ke dab da tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, inda kusan mutane 50 suka mutu a halin yanzu. Wannan ya zama karo na biyu da aka samu kifewar jirgin ruwa da ke dauke da bakin haure a tekun tsibirin Lampedusa a cikin rabin watan guda

Bisa labarin da muka samu, an ce, wannan hadari ya faru ne da misalin karfe 5 da mintoci 15 na yamma, kimanin mil 60 daga kudancin tsibirin Lampedusa, bisa kwarya-kwaryan bincike da aka yi, an ce jirgin ruwan ya kife ne sakamakon mutane fiye da kima da ya kamata ya dauka. Rahoton ya ce, ya zuwa yanzu wannan hadari ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 50, ciki har da yara 10.

Gwamnatin Italiya ta bayar da wani labari a wannan rana cewa, firaministan kasar Enrico Letta ya riga ya yanke shawarar gabatar da matsalar bakin haure da ke kokarin shiga kasar ta barauniyar hanya a taron koli na kungiyar EU, wanda za a shirya a karshen watan nan.

A ranar 3 ga watan nan ma, wani jirgin ruwa da ke dauke da bakin haure fiye da 500 ya nitse a yankin tekun da ke dab da tsibirin Lampedusa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 363, kuma har yanzu ba a gano wasu mutanen ba. Wannan hadari ya girgiza baki dayan nahiyar Turai, shugaban kwamitin kungiyar EU Jose' Manuel Barroso ya ziyarci tsibirin Lampedusa a 'yan kwanakin baya, inda ya ce, EU za ta ba da taimakon da ya dace ga Italiya, wajen tinkarar matsalar kwararar bakin haure ba bisa ka'ida ba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China