Kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika ( UEMOA) dake kunshe da kasashe takwas ta amince a ranar Jumma'a a birnin Dakar na kasar Senegal tsarin shirin zaman lafiya da tsaro a wannan shiyyar tattalin arziki da kudi, a wani labarin kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Ministocin harkokin waje, da na tattalin arziki da kudi, da na tsaron kasashe mambobin kungiyar UEMOA sun cimma wannan shirin bayan wani zaman taro na kwamitin manyan jami'ai domin aiwatar da aikin zaman lafiya da tsaro na kungiyar UEMOA, da shugaban kasar Senegal, Macky Sall ke jagoranta.
A cewar ministan harkokin wajen kasar Senegal, Mankeur Ndiaye, wannan shirin na mai da hankali wajen sanin musabbabin tashe tashen hankali, har ma kuma da manyan hanyoyin biyu na yin rigakafi da kulawa da ricike rikice.
A cewar mista Ndiaye, aiwatar da wannan shirin na da makasudin bullo da manyan manufofin siyasa cikin hadin gwiwa ta fuskar zaman lafiya da tsaro cikin tunanin taimakawa juna tare da dukkan kungiyoyin dake tasirin a shiyyar. (Maman Ada)