Shugabannin kasashen kungiyar tattalin arziki da kudu ta yammacin Afrika (UEMOA) sun gudanar a ranar Litinin a birnin Ouagadougou da bukukuwan cikon shekaru 20 na wannan hukuma a karkashin taken manyanta da sabbin kalubalolin da za'a cimma. Kungiyar EUMOA na kunshe da kasashe takwas dake amfani da kudin Sefa, wadanda suke hada da Benin, Burkina-Faso, Cote d'Ivoire, Guinea-Bissau, Mali, Niger, Togo da Senegal. Shugaban kwamitin UEMOA, shugaban kasar Senegal Cheik Adjoubou Soumare, ya bayyana cewa, bikin cikon shekaru 20 ya kasance wata dama domin gabatar da cigaban dunkulewar shiyyar, yin nazari kan nasarorin da aka samu da kuma matsalolin da aka fuskanta a tsawon wadannan shekaru 20.
A tsawon tsarinta na tattalin arzikin shiyyar (PER), kungiyar UEMOA ta zuba jari na Sefa fiye biliyan 306 wato kwatankwacin dalar Amurka miliyan 612 domin gina manyan ayyuka fiye da 163 a nahiyar Afrika.
A nasa bangare, shugaban taron shugabannin kungiyar a wannan karon, shugaban kasar Benin Boni Yayi ya jaddada cewa, dunkulewar tattalin arziki shi ne mataki mafi karfi wajen yaki da talauci da kuma ingiza ci gaba. Zirga zirgar kayayyaki da jama'a cikin 'yanci shi ne ginshikin cigaba, in ji Boni Yayi. (Maman Ada)