in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu ruwa da tsaki na nuna kwarin gwiwa game da ci gaban da Sin za ta samar a nahiyar Afirka
2015-12-10 13:19:35 cri
Masana da masu fashin baki da dama sun bayyana ra'ayoyin su game da irin ci gaba da manufofin kasar Sin ka iya haifarwa ga al'ummomin nahiyar Afirka, musamman ma game da sakamakon taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC wanda ya kammala a karshen makon jiya.

Farfesa Frank Youngman daga kasar Botswana, wanda kuma masani ne game da dangantakar Sin da Afirka, ya bayyana cewa sabbin manufofin da Sin ta gabatar yayin taron dandalin FOCAC, za su yi matukar tasiri wajen habaka tattalin arzikin sassan biyu. Ya ce akwai bukatar Botswana ta zage damtse wajen cin gajiyar wadannan manufofi na ci gaba.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zayyana wasu matakai 10 da kasar sa za ta dauka, wajen inganta hadin gwiwar ta da nahiyar Afirka cikin shekaru uku masu zuwa. Kaza lika shugaba Xi ya bukaci sassan biyu da su maida hankali, wajen karfafa wasu ginshikan ci gaba guda 5, ta yadda za su samu damar cin gajiyar kawancen su yadda ya kamata.

Da yake karin haske game da hakan, Farfesa Youngman ya ce tun kafuwar dandalin FOCAC a shekara ta 2000, mahukuntan kasar Sin na amfani da tazarar shekaru uku-uku, wajen bayyana manufofi, da kuma kudurori, tare da samar da kudaden gudanar da sabbin shirye shiryen fadada hadin gwiwa da nahiyar Afirka. Mr. Youngman wanda ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya kara da cewa taron FOCAC na bana wanda ya gudana a Afirka ta Kudu, ya zo a gabar da masu ruwa da tsaki da manazarta ke dakon sa.

A cewar sa, karkashin manufar aiwatar da tsare-tsaren da aka sanya gaba, Sin ta alkawarta samar da kudi har dala biliyan 60 a matsayin tallafin samar da nau'o'in rance daban daban, kudin da suka haura adadin da aka yi tsammani, wanda hakan ya nuna irin muhimmancin da kasar ke baiwa alakar ta da kasashen nahiyar Afirka.

Sassan da Sin din za ta maida hankali a kan su dai sun hada da bunkasa masana'antu, da zamanantar da aikin gona, da samar da manyan ababen more rayuwa, da inganta hada-hadar kudade, da kuma amfani da fasahohin da ba sa gurbata muhalli. Sauran sun hada da fannin cinikayya da zuba jari, da yaki da talauci, da kyautata rayuwar jama'a, da inganta fannin kiwon lafiya. Sai kuma fannin musayar fasahohi tsakanin al'ummomin sassan biyu, da kuma hadin gwiwa wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Farfesa Youngman ya kara da cewa muhimmai cikin wadannan manufofi su ne batun bunkasa masana'antun Afirka, da kuma musayar fasahohin ci gaba, wadannan a cewar sa ginshikai ne da za su matukar daga matsayin nahiyar Afirka. Ko shakka babu a cewar wannan masani, alakar dake tsakanin Sin da Afirka ta shiga wani sabon matsayi na bunkasuwa. Sai dai a daya hannu ya zama wajibi sassan biyu su maida hankali wajen ganin an cimma nasarorin da aka sanya gaba nan da shekaru ukun dake tafe.

Shi ma a nasa tsokaci game da wannan batu, mataimakin shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi, cewa ya yi kasar sa za ta ci gajiya mai gwabi daga tanaje-tanajen da kasar Sin ta zayyana yayin taron FOCAC na bana. Mr. Masisi wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarun kasar sa wato BOPA bayan halartar taron na FOCAC, ya kara da cewa a wannan gaba da Sin ke dada samar da lamuni mai sauki domin bunkasa samar da manyan ababen more rayuwa, a nata bangare gwamnatin Botswana na daukar matakan fadada hanyoyin bunkasa tattalin arzikin ta, za kuma ta tabbatar da cin gajiyar rancen da Sin ta gabatar domin kasashen na Afirka.

A wani ci gaban kuma, wani masanin tattalin arziki a kasar ta Botswana Dr. Keith Jefferies, cewa ya yi dole ne kasar sa ta hada kai da Sin, don ganin ta ci gajiyar dabarun bunkasa samar da ababen more rayuwa, da kuma sauran fasahohin zamani. Dr. Jefferies ya ce hakan ya zama wajibi idan aka yi la'akari da kasancewar Botswanan kasa dake matsayin wata cibiya ta masana'antu, da cinikayya, da kuma hakar ma'adanai a yankin kudancin Afirka. Bugu da kari Jefferies ya bayyana hadin gwiwar Sin da Afirka a matsayin wani mataki wanda muddin aka inganta shi, zai zamo jigon bunkasar kasashen nahiyar baki daya, musamman idan aka gudanar da ayyukan, karkashin inuwar kungiyoyi da hukumomin shiyyoyin nahiyar kamar kungiyar SADC da ECOWAS.

Dr. Jefferies ya ce Botswana na daukar Sin a matsayin aminiya ta kut da kut a fannin ci gaba, wanda kuma ke amfani da huldodin ta na diflomasiyya wajen ganin an cimma burikan da aka sanya gaba, tun daga shekarar 1975, lokacin da sassan biyu suka kulla alakar kawance.(Saminu Alhassan)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China