A yau Talata, an bude taron koli na kafofin watsa labaru na kasashen BRICS karo na farko a nan birnin Beijing. Ministan kula da harkokin yada labarai na kasar Sin Liu Qibao ya halarci taron tare da ba da jawabi, inda ya jaddada cewa, ya kamata a nace ga manufar BRICS ta bude kofa da yin hadin gwiwa da kawo moriyar juna, da kara musayar ra'ayi da hadin gwiwa, da nufin kafa makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na kasashen BRICS.
Kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin shi ne ya kira wannan taro tare da kamfanin watsa labaru na kasar Brazil da kuma kamfanin dillancin labaru mai suna 'Today' na kasar Rasha da jaridar Hindu ta kasar India da kamfanin watsa labaru mai zaman kansa na kasar Afrika ta kudu. (Lami)