in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gabatar da jerin sabbin matakan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a taron dandalin FOCAC
2015-11-27 15:20:34 cri

A bana ne ake cika shekaru 15 da kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika na FOCAC, inda za a gudanar da taron koli tare da taron ministoci karo na shida na dandalin a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu a farkon wata mai zuwa.

Wannan ne dai karo na farko da aka kira taron kolin na FOCAC a nahiyar Afrika, wanda zai sami jagoranci daga shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Afrika ta Kudu Jacob Zuma, inda kuma za a gabatar da jerin sabbin matakai dake da nasaba da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika.

A jiya Alhamsi, wani jami'i na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ya bayyana cewa a nan gaba, Sin da Afrika za su mai da hankali kan hadin gwiwa a wasu manyan fannoni, ciki hadda taimaka wa Afirka wajen raya masana'antu, da aikin gona na zamani, gami da manyan ababen more rayuwa da dai sauransu.

An kafa dandalin FOCAC ne a shekara ta 2000. Yayin da ake gudanar da taron ministoci karo na biyar a shekarar 2012, kasar Sin ta sanar da baiwa Afirka taimako a manyan fannoni biyar, da sa kaimi ga raya sabuwar dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Afrika.

Yayin wani taron manema labaru da majalissar gudanarwa ta kasar Sin ta gudanar a jiya, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Mista Qian Keming, ya nuna cewa Sin ta cimma burinta na baiwa kasashen Afirka rancen kudi, wanda yawansa ya kai fiye da dala biliyan 20 a cikin shekaru 3 da suka gabata, baya ga gudanar da ayyukan taimako fiye da 900, tare da horar da 'yan Afirka masu rike da fasahohi daban daban fiye da dubu 30. Ban da wannan kuma, Sin ta ba da taimako wajen shimfida layin dogo tsakanin birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha da birnin Djibouti, da layin dogo tsakanin biranen Mombasa da Nairobi dake kasar Kenya, da dai sauran ayyuka makamantan hakan.

Mista Qian Keming, ya ce Sin ta baiwa kasashen Afirka tallafin jin kai, da taimakon jin dadin jama'a ne bisa ka'idar taimakawa juna, da kawo moriyar juna gwargwadon karfinta. Yayin da yake magana kan hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da ciniki tsakanin sassan biyu, Mista Qian ya ce,

"Kasar Sin ta kasance abokiyar Afirka mafi girma wajen cinikayya a shekaru shida da suka gabata a jere, inda yawan kudi dake shafar wannan fanni ya kai dala biliyan 222 a shekarar 2014, adadin da ya ninka sau 20 idan an kwatanta da farkon lokacin kafuwar FOCAC. Afirka kuwa ta zama kasuwa ta biyu a duniya da Sin ke gudanar da ayyukan kwangila, baya ga wuri mai muhimmanci da Sin ta zuba jarinta. Ya zuwa karshen shekarar bara, yawan kudin da Sin ta zuba kai tsaye a Afrika, ya kai dala biliyan 32.4, kana matsakaicin yawan saurin karuwa da aka samu a wannan fanni ya zarce kashi 30 bisa dari a cikin shekaru 15 da suka gabata. Hakan ya sa, Sin da Afirka ke kara samun bunkasuwa ta fuskar hadin gwiwa a fannoni daban-daban, ciki hadda aikin gona, da sha'anin samar da kayayyaki, da hada-hadar kudi, da yawon shakatawa, da zirga-zirgar jiragen sama. Sauran fannonin sun hada da na sadarwa, da gidan rediyo da na talibiji, da kiwon lafiya da ba da jiyya, da sufurin kayayyaki da sauransu.".

Ciniki tsakanin Sin da Afrika na fuskantar koma baya, sakamakon tafiyar wahainiya da bunkasar tattalin arziki na kasashen duniya ke fuskanta tun daga farkon wannan shekarar da muke ciki. Game da wannan batu, Mista Qian ya ce jimillar cinikayya tsakanin Sin da Afrika ya ragu ne, bisa dalilin faduwar farashin manyan kayayyaki a duniya. Yawan kayayyakin da Sin ke shigo da su daga Afrika bai ragu ba, hasali ma dai yawan wasu kayayyakin da Sin ke shigowa da su daga Afrika na karuwa. A sa'i daya kuma, yawan kudin da Sin ta samu ta fuskar fitar da kayayyaki zuwa Afrika ya karu, duk da raguwar cinikayya da duniya ke fuskanta. Wannan adadi ya kai dala biliyan 80.9, wanda ke nuna an samu karuwa da kashi 5.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci a bara, matakin da ya alamta cewa, Afrika na da matukar bukatar kayayyaki daga kasar Sin. Idan mu yi hange nesa, za mu ga akwai makoma mai kyau game da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ta fuskar cinikayya a nan gaba, kuma sassan biyu za su samarwa juna moriya bisa bukatunsu.

Game da yiwuwar samun kyautatuwa a tsakanin bangarorin biyu, Mista Qian ya ce.

"Akwai matsalar rashin samun daidaito tsakanin Sin da Afrika ta fuskar cinikayya, duba da cewa Sin ta samun rarar kudi, yayin da kuma Afrika ke samun gibin cinikayya. Wata matsala ta daban ita ce, nau'o'in kayayyakin da Sin ke shigo da su daga Afrika ba su da yawa, wato ba su wuce makamashi da wasu kaya na amfanin gona ba. Don haka, Sin za ta kyautata wannan hali ta hanyar kara shigo da sauran kayayyaki daga Afrika. A wani bangare kuwa, Sin za ta habaka zuba jari a Afrika, musamman ma a fannin masana'antu da sha'anin samar da kayayyaki, da inganta hadin gwiwa a wannan fannin, ta yadda ciniki tsakaninsu zai samu bunkasuwa mai dorewa."

Za a kira taron koli na Johannesburg kuma taron ministoci karo na shida na FOCAC a farkon watan Disamba a Afrika ta Kudu, kuma wannan zai kasance karo na farko da za a kira irin wannan taro a nahiyar Afrika, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron tare da gabatar da jawabi. Bugu da kari ana sa ran za a gudanar da bikin baje koli na na'urorin masana'antu na Sin da Afirka, kana da taron tattaunwa tsakanin shugabannin Sin da Afrika tare da wakilan masu masana'antu da 'yan kasuwa a yayin taron dandalin FOCAC. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China