in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika na fuskantar sabon zarafi
2015-11-26 19:28:15 cri
Da safiyar yau Alhamis, kafin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi zuwa kasar Afrika ta kudu don halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika a birnin Johannesburg, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta kira taron manema labaru a nan birnin Beijing, inda ministan harkokin waje na kasar Wang Yi, ya yi jawabi kan huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, wadda a cewar sa za ta samu sabuwar bunkasuwa, domin bayyana sabbin abubuwa dangane da hadin gwiwar bangarorin biyu a karkashin sabon tsari.

A yayin da yake jawabi kan yadda aka zabi kasar Afrika ta kudu don karbar bakuncin taron kolin na wannan karo, Wang Yi ya bayyana cewa, "Shugabannin kasashen Afrika da dama sun gabatarwa kasar Sin bukatar su na daga matsayin taron minista na dandalin tattauna hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika zuwa taron koli, shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma wanda shine mai masaukin baki, ya gayyaci shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa kasar don ba shi damar karbar bakuncin taron kolin.

Shugaba Xi ya amshi goron gayyatar inda ya yanke shawarar halartar taron, domin sada zumunta da musayar ra'ayi kan hadin gwiwa da neman samun bunkasuwa tare da shugabannin kasashen Afrika, ta yadda za su daga matsayin huldar hadin gwiwa a tsakaninsu."

A halin yanzu, an kammala ayyukan share fagen taron koli na Johannesburg. Shugaba Xi Jinping zai gabatar da jawabi a yayin bikin budewar taron kolin, inda zai yi bayanai game da sabon tunani da manufofi da ra'ayoyin Sin na raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka, musamman gabatar da sabbin matakan kara hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Kana za a yi bincike kan takardu guda biyu a gun taron, inda za a tsara ayyukan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a shekaru uku masu zuwa. Game da wannan, Wang Yi ya bayyana cewa, "Taron kolin a wannan karo, zai kasance taron zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Sin za ta gabatar da sabbin matakan kara hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a dukkan fannoni bisa bukatun hadin gwiwarsu na yanzu. Za a dora muhimmanci kan manyan ayyukan gaggauta raya masana'antu da aikin noma a Afirka, da warware matsalolin rashin ingantattun ababan more rayuwa, da kara taimakawa kasashen Afirka wajen kafa tsarin raya masana'antu, da samar da abinci, da tabbatar da kiwon lafiya da magance cututtuka don warware matsalolin samar da guranban aikin yi, abinci da kuma kiwon lafiya a nahiyar."

Game da makoma mai kyau da taron koli zai kawo ma hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, jakadar kasar Afrika ta kudu dake kasar Sin Madam Dolana Msimang ta nuna kyakkyawan fatanta, ta ce, "Hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya gabatar da wata hanya mai kyau ga bunkasuwar nahiyar Afrika, a gani na, kasar Sin aminiya ce ga kasashen Afrika, wadda ba za a ta iya maye gurbinta ba ko kadan. Ta yin amfani da wannan zarafi mai kyau, a madadin gwamnatin kasar Afirka ta kudu, muna nuna godiya sosai ga taimakon da Sin take bamu wajen raya nahiyar mu. Kuma na yi amanna cewar, taron zai samun ci gaba mai armashi, kuma wannan matakin zai amfanawa jama'ar kasashen Sin da Afrika."

Amma duk da haka, wasu kafofin duniya sun nuna shakku da damuwa kan yadda huldar hadin gwiwar Sin da Afirka take samun ci gaba cikin sauri. Dangane da haka, mista Wang Yi ya ce, hadin kan bangarorin Sin da Afirka yana haifar da moriya ga junansu.

"Ana hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ne bisa zaman daidaituwa da son rai, don haka yayin da kasar Sin take hulda da kawayenta dake nahiyar Afirka, ba ta taba gindaya wani sharadi siyasa ba, ba ta taba tilastawa wani don ya aikata abin da ba son ransa ba, ba ta taba tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen Afirka ba, sannan a koda yaushe tana cika alkawuran da ta dauka. Wadannan abubuwa, ba wanda zai fi jama'ar kasashen Afirka sanin gaskiyar su. Duk wanda ke son shafa kashin kaza ga hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka, ba zai yi nasara ba, domin muna da shaidu da yawa da za su shaida cewa maganarsa karya ce, jama'ar Sin da na kasashen Afirka ba za su taba yarda da duk wata yaudara ko yi musu sakiyar da ba ruwa ba." (Lami, Zainab, Amina, Bello, Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China