in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tabbatar wa 'yan sandan Liberiya da ci gaba da ba da goyon bayanta
2015-11-24 10:52:06 cri

Gwamnatin kasar Sin a ranar Litinin ta ce, za ta ci gaba da ba da goyon bayanta ga 'yan sandan kasar Liberiya a ayyukanta na tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar UNMIL.

Jakadan kasar Sin a Liberiya Zhang Yue a cikin wata sanarwa da ya fitar wa Xinhua ya tabbatar da cewa, Sin za ta ci gaba da goyon baya tare da hada kai da Liberiyan wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

Sanarwar ta yi bayanin cewa, jakadan na kasar Sin ya tabbatar da hakan ne lokacin da ya mika kayayyakin da suka hada da baburan 'yan sanda guda 30, manyan motocin jeep kirar kasar Sin guda 2 da sauran kayyayaki na hana tashin tarzoma ga rundunar 'yan sandan kasar, wadanda darajarsu ta kai kimanin kudin Sin RMB miliyan 1.3.

Wakilin na kasar Sin ya sanar da cewa, gudunmuwar kayayyakin ta biyo bayan bukatar da rundunar 'yan sandan kasar Liberiya ta mika ne ga ma'aikatar tsaron al'umma ta kasar Sin.

Babban sipeton 'yan sandan kasar Kanar Chris C Massaquoi a lokacin da yake karban kayayyakin, ya yaba wa gwamnatin kasar Sin bisa ga wannan gudunmuwa, yana mai lura cewa, kayayyakin za su taimaka wa 'yan sandan kasar matuka wajen shawo kan kalubalolin da suke fuskanta ta bangaren tsaro a kasar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China