in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin MDD na Sin fiye da 500 suna aiki a Liberiya
2015-11-03 10:05:09 cri

Fiye da sojojin MDD na kasar Sin fiye da 500 ne sun shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya daban daban a kasar Liberiya, kuma aikinsu ya samu yabo sosai daga wani babban jami'in MDD.

Zan iya ba su makin 9 bisa na 10, wata kila ma 10 bisa 10, in ji Hubert H. Price, darektan ayyuakan tawagogin MDD dake Liberiya, yayin da yake bayyana ra'ayinsa kan aikin wadannan dakarun zaman lafiya na kasar Sin.

A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar 29 ga watan Oktoba, jami'in ya kimanta aikin sojojin MDD na kasar Sin da kwarewa sosai da kuma da'a, tare da bayyana cewa, sun taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a Liberiya.

Rukunonin sufuri, injiniya da likitanci na kasar Sin suna aiki cikin wahala domin tabbatar da yanayin cudanya mai kyau tare da al'ummomin wurin.

Sin ta kara yawaita kokarinta na tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya a tsawon shekaru fiye da goma da suka gabata.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar a cikin watan Satumban da ya gabata, a yayin babban taron MDD, cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa, Sin za ta kebe dalar Amurka miliyan 100 domin taimakawa nahiyar Afrika kafa rundunarta.

Har ila yau, kasar Sin za ta tura rukuninta na farko na jirage masu saukar ungulu a cikin tawagogin wanzar da zaman lafiya na MDD a nahiyar Afrika.

Mista Price ya bayyana cewa, tallafin da kasar Sin ke baiwa kungiyar tarayyar Afrika (AU) zai taimaka sosai wajen kyautata karfin AU wajen magance rikice rikice da fuskantar kalubalolin a nan gaba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China