in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude baje kolin kayayyakin Sin a yammacin Afrika karo na 7 a Cotonou
2015-08-26 12:52:24 cri

Bajen koli na kayayyakin kasuwanci na kasar Sin a yammacin Afrika karo na bakwai wanda ke da nufin baiwa manyan 'yan kasuwa na Afrika damar ganin muhimman albarkatun tattalin arziki da kasar Sin take da su a fannin kayayyaki da ayyuka, ya bude kofa a ranar Talata a Cotonou, hedkwatar tattalin arzikin kasar Benin.

Ma'aikatar kasuwanci ta Sin da ta Benin suka shirya wannan baje koli cikin hadin gwiwa, baje kolin ya zama wani muhimmin dandali na gabatar da kayayyakin Sin zuwa kasuwannin Benin da na kasashen yammacin Afrika.

Haka kuma wata dama ce ga manyan 'yan kasuwar Benin da na kasashen yammacin Afrika da su kulla dangantakar kasuwanci da kwarewa tare domin kara samun moriya.

Baje koli na kayayyakin Sin a yammacin Afrika da ke gudanarwa a kasar Benin ya kasance wani babban dandali na kasa da kasa da aka shirya a Benin, kuma ya samu halartar 'yan kasuwa na 'yammacin Afrika, tsakiyar Afrika, da na gabashin Afrika.

Da take jawabi a yayin bikin bude wannan bajen koli, ministar kudin Benin, madam Naomie Azaria, dake maye gurbin takwaranta na kasuwanci, ta bayyana cewa, wannan baje kolin kayayyakin Sin a kasar Benin na karfafa dangantakar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Sin da kasashen Afrika, da kuma baiwa 'yan kasuwa na Afrika da yawa damar zuwa kasar Sin domin harkokin kasuwanci .

Wannan dandalin kasuwanci ya amsa muhimman bukatun 'yan kasuwa na Afrika, har ma da na al'ummar Afrika baki daya, in ji madam Azaria. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China