in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban taron Sin da Afrika zai tabo garambawul a kasuwanci da zuba jari
2015-11-11 10:28:11 cri

Jami'an kasashen Sin da Kenya sun fada a ranar Talatar nan a Nairobi cewar, babban taron shugabannin Sin da Afrika wanda ake sa ran gudanarwa a ranakun 4 da 5 ga watan Disamba a Johannesburg, zai tabo batun yin gyaran fuska a fannin tattalin arziki da dangantaka tsakanin bangarorin biyu.

Da yake jawabi a yayin halartar taron karawa juna sani mai taken karfafa dangantaka tsakanin Sin da Afrika, jakada Ji Peiding, wakili a ma'aikatar harkokin wajen Sin ya ce, dandali na Sin da Afrika wato FOCAC, zai taimaka wajen samar da daidaito, da kuma sake karfafa kyakkyawar dangantaka tsakanin bangarorin biyu.

Taron wanda na hadin gwiwa ne da cibiyar tsara dabaru ta Afrika, zai yi nazarin sahihan hanyoyin da za'a bi domin daidaita yanayin dangantakar Sin da Afrika a sha'anin tattalin arziki.

Peter Kagwanja na cibiyar tsara dabaru ta Afrika ta Kenya ya ce, kasar Sin ita ce babban jigo na samar da kudaden raya ci gaban nahiyar Afrika, musamman saboda yadda kasar ke zuba makudan kudade a harkokin cinikayya da inganta samar da kayayyakin da masa'anantu ke amfani da su a kasashen na Afrika.(Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China