Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon, ya samu goron gayyata domin halarta bikin cikon shekaru 25 da samun 'yancin kasar Namibiya da kuma bikin rantsar da shugaban kasar na uku, Hage Geingob a ranar Asabar mai zuwa a Windhoek.
Ya zuwa dai wannan ranar, shugabannin kasashe goma ne suka tabbatar da zuwansu a bikin da za a shirya a babban filin wasan kasar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, gwamnatin kasar ta bayyana cewa, za a tabbatar da tsaron dukkan shugabannin kasashen da aka gayyato, kuma ba za su bukatar zuwa da jami'an tsaronsu da za su kiyaye lafiyarsu ba. (Maman Ada)