Wani sakamakon bincike na baya bayan nan wanda aka wallafa shi a Larabar nan, ya gano cewar, kwayoyin cutar Ebola za su iya rayuwa a cikin maniyin dan adam har na tsawon watanni 9.
A baya dai, ana iya gane cutar Ebola a maniyin maza ne, amma babu wani takamamman ilmi dangane da tsawon lokacin da kwayar cutar za ta iya rayuwa a jikin mutum.
A sabon binciken da aka gudanar, an yi gwajin kwayoyin cutar ne a maniyin da maza 93 'yan shekaru sama da 18 dake dauke da cutar a birnin Freetown na kasar Saliyo suka samar.
Sakamakon gwajin da aka yi a kan wasu mutanen, an gano kwayoyin cutar a jikin su bayan sun shafe watanni 3 dauke da cutar daga lokacin yin gwajin, kamar yadda aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya wato New England Journal of Medicine.
Sakamakon gwajin ya tabbatar da cewar, daga wata 4 zuwa 6 kusan rabin mutanen da aka gwada ne ke dauke da cutar, sannan bayan tsakanin watanni 6 zuwa 9 daya bisa uku ne na mutanen da suka kamu ke dauke da kwayar cutar.(Ahmad Fagam)