in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gadajen jinyar masu dauke da Ebola sun magance mutuwar marasa lafiya 40,000 a Saliyo
2015-10-14 10:06:12 cri

Samar da gadaje na musamman domin jinyar masu dauke da cutar Ebola ya hana mutane kimanin 57,000 su kamu da cutar, kuma ya magance mutuwar masu dauke da cutar 40000 a kasar Saliyo, kamar yadda wani sabon bincike ya nuna.

Binciken ya nuna cewa, saurin daukar mataki daga ciki da wajen gida ya yi matukar rage karuwar barkewar cutar kamar yadda jagorar binciken Author Adam Kucharski na makarantar horon jinya da likitanci a Ingila ya bayyana cikin wata sanarwa.

Ya ce, ganin yadda cutar ta yi saurin barkewa a kasar ta Saliyo, inda a ce idan ba'a samar da wadannan gadajen jinyar, aka kebe majinyatar, tare da hana yaduwar cutar ba, annobar za ta fi haka tsanani.

Kididdiga daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ta nuna cewa, an samu kusan wadanda suka kamu da cutar 13,945 a kasar ta Saliyo ya zuwa yanzu kuma kusan kashi 70% suka mutu a shekarar bara. Sannan akwai wadanda suka kamu da cutar da dama da ba'a rahoton su ba, in ba haka ba, ainihin adadin zai fi haka.

A tsakanin watan Satumbar bara zuwa Fabrairun bana, an samar da gadajen jinya fiye da 1,500 a cibiyoyin jinyar masu dauke da cutar dake ko ina a sassan kasar, sannan kuma za a kara samar da gadajen 1,200 domin ba da taimako ga asibitocin kasar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China