Sakatare janar yayi allawadai da hare haren bam da suka faru a karkarar Abuja a ranar 2 ga watan Oktoba haka kuma da wasu jerin fashewa da suka faru a Maiduguri babban birnin jihar Borno, hare haren da aka danganta su da kungiyar Boko Haram, in ji kakakin Ban Ki-moon a cikin wata sanarwa.
Ayyukan tashin hankali da kungiyar Boko Haram take kai wa sun kasance wani babban tarnaki ga 'yancin kasa da kasa, ga bil adama da kuma addini, a cewar wannan sanarwa.
Mutane 18 suka mutu yayin da wasu 41 suka jakkata a cikin fashewar boma bomai uku a Abuja.
Wadannan hare haren sun faru a washegarin bala'in da ya afkawa Maiduguri, inda wasu jerin fashewar boma bomai suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 14 da jikkata 39.
Mista Ban ya aike da ta'aziyyarsa ga iyalan da wadannan hadura suka rutsa dasu da kuma gwamnatin Najeriya, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata, a cewar wannan sanarwa.
Haka kuma, mista Ban ya sake jaddada goyon bayan MDD ga gwamnatin Najeriya bisa kokarin da take wajen yaki da ta'addanci. (Maman Ada)