in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiya ta samu masu dauke da cutar MERS guda 6 a mako daya
2015-07-06 10:00:03 cri

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Saudi Arabiya ta sanar a ranar Asabar din nan cewa, ta samu masu dauke da annobar nan da ake kira MERS su 6 a mako daya tun daga ranar 28 ga watan Yuni zuwa 4 ga wannan watan na Yuli.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya ruwaito, ya zuwa yanzu, an samu masu dauke da cutar har 1,045 da a cikin su guda 460 sun mutu. Kasar ta dauki matakai masu tsanani wajen ba da kariya da kuma kulawa da wadanda suka kamu da cutar, inda ake samu wadanda suka warke da kashi 55.3%.

An samu sabbin masu dauke da cutar shida ne a Riyadh da Damam lokacin da aka yi gwaji a kan samfuri 644 a dakin gwajin kwayoyin halittu a makon jiya.

Tun farkon barkewar annobar ta MERS a shekara ta 2012, kasar ta Saudiya sau biyu tana canza ministocin kiwon lafiyarta, sannan mahukuntar kiwon lafiyar kasar sun gargadi al'ummarsu da su kaurace wa cin nama, ko shan madarar rakumi wanda shi ne babban abin da ake zargin yake yada cutar cikin hanzari.

A cewar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, daya daga cikin alamun kamuwa da cutar shi ne zazzabi, tari da katsewar numfashi wanda zai iya jawo ciwon sanyin hakarkari ko kuma lalacewar kodar dan adam.

Wannan kwayar cuta dai ana samun ta ne a tsakanin jama'a wadanda suka kamu da ita ko kuma ta hanyoyin amfanin da kayayyakin kiwon lafiyar da aka yi wa wadanda suka kamu da cutar aiki kamar a asibiti, ko kuma hulda kai tsaye da rakumai. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China