in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira ga Somaliya da ta ci gaba da gina dunkulalliyar kasa ta demokradiya
2015-09-29 10:18:21 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ce, Somaliya ta samu ci gaba cikin tsanaki wajen gina dunkulalliyar kasa ta demokradiya, sai dai ya kamata ta ci gaba da kokari a kan hakan.

Mr Ban ya fadi hakan ne a lokacin wata tattaunawa ta musamman a kan kasar ta Somaliya da aka yi a hedkwatar majalissar dake birnin New York.

Ya ce, an ga kafuwar gwamnatin wucin gadi, kaddamar da shirin gyara a kan kundin tsarin mulki, da kuma kirkiro sabuwar hukumar zabe mai zaman kanta. A baya bayan nan ma ya ce, ya yi maraba da kaddamar da babban taron sulhuntawa da aka yi a ranar 19 ga wata domin amincewa da shirin zabe na shekara mai zuwa wanda a cewar shi wadannan muhimman matakai ne sai dai akwai bukatar ganin sun dore.

Mr Ban daga nan sai ya tunatar da cewa, Somaliya ba za ta iya yarda ta kauce hanya ba saboda siyasar gefe daya ko ta son kai, don haka ya kara kira ga masu ruwa da tsaki da su yi aiki tare a kan burin da ake neman a cimmawa da suka hada da kafawa da sake nazarin kundin tsarin mulki, da kuma tabbatar da shiga da kowa cikin ayyukan zaben na shekara ta 2016.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China