in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mayakan Al-Shabaab 12 a kudancin Somaliya
2015-08-26 10:05:13 cri

Shedun gani da ido da kuma hukumomin gwamnati a kasar Somaliya sun ce, an hallaka mayakan kungiyar Al-Shabaab kimanin 12 yayin wani artabu tsakanin dakarun gwamntin kasar da mayakan na Al-Shabaab a ranar Talatar nan a kusa da kauyen Garbaherey dake yankin Gedo a kudancin Somaliya.

Kwamandan rundunar sojan kasar dake yankin Gedo Abdullahi Osman ne ya tabbatar da hakan ga manena labaru, ya ce, dakarun gwamnatin sun kai wani kazamin hari ne a kauyen Tula Barwako.

Ya kara da cewar, sun kashe mayakan na Al-Shabaab kimanin 12, kuma sun samu nasarar kwace makamai daga hannun mayakan, sai dai a cewarsa, soja guda ya samu raunuka, kuma a yanzu haka sojojin ne ke rike da iko a kauyen.

Kwamandan ya ce, tuni mayakan suka tsere cikin daji bayan da fadan ya kazanta, kuma wasu mazauna yankin sun ce an shafe tsawon sa'o'i ana gwabza fadan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China