in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana wasan motsa jiki don zurfafa zumunci tsakanin Sin da Ghana
2015-08-25 10:05:31 cri

Kungiyar sada zumunci tsakani Sin da Ghana ta shirya wasannin motsa jiki domin murnar shekaru 55 da fara huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu, inda al'ummomin kasashen biyu suka fafata a wasan kwallon kwando da kwallon tebur wanda ya samu halartar 'yan kallo da dama a Accra, babban birnin kasar.

Ghana dai ita ce daya daga cikin kasashen Afrika da Sin ta kulla huldar diplomasiya da ita. Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin, akwai jakadar kasar Sin a Ghana Sun Baohong, ministan wasanni na Ghana Mustapha Ahmed, da kuma ministan lafiyar kasar Alex Segbefia.

A jawabin ta jakada Sun Baohong, ta ce, zumunci tsakanin kasashen biyu wani muhimmin matsayi ne dake ci gaba da rike da abin da ya faru a baya, tare da kawo na gaba cikin yakini. A don haka ta bukaci bangarorin biyu da su kara himma a kan yanayin da ake ciki yanzu wajen fadada musanyar al'adu, da kuma kara samo dabaru da hanyoyin da za'a karfafa zumunci tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

A nashi jawabin, minista Mustapha Ahmed ya ce, wasannin da ake yi za su taimaka wajen karfafa zumunci tsakanin Ghana da Sin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China