in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya tsawaita wa'adin aikin tawagar UNMIL
2015-09-18 09:52:07 cri

Kwamitin tsaron MDD, ya tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNMIL mai gudanar da ayyukan ta a Liberia, ya zuwa ranar 30 ga watan Satumbar badi.

Hakan dai ya biyo bayan cimma wani kuduri da wakilan kwamitin 15 suka yi, a wani mataki na tabbatar da nasarar dakile kalubalen tsaro, da tabbatar da yanayin zaman lafiya mai dorewa a Liberia, da ma daukacin yankin da take.

Sabon kudurin kwamitin na tsaron ya kuma jinjinawa hadin gwiwar dake wakana tsakanin gwamnatin kasar ta Liberia da tawagar ta UNMIL, musamman game da shirin su na damkawa Liberian ragamar ayyukan tsaron ta a ranar 30 ga watan Yuni shekarar ta badi.

Har ila yau, kwamitin ya jaddada burin ganin mahukuntan Liberian sun sauke nauyin dake wuyansu game da cimma wannan buri a kan lokaci. A daya hannun kuma ya bukaci tawagar wanzar da zaman lafiyar da ta ci gaba da baiwa kasar tallafi, a fannin sanin makamar aiki, da ma sauran dabarun cimma nasarar da aka sanya gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China