in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na kasar Sin sun tashi zuwa Liberiya
2015-09-08 10:29:53 cri
Rukunin ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na kasar Sin kimanin 257 sun tashi daga birning Beijing a ranar Litinin din nan don gudanar da ayyukan MDD na watanni 12 a kasar Liberiya.

Wadannan rukuni su ne na farko cikin rukuni 18 na ma'aikatan kiyaye zaman lafiya daga kasar Sin da suka fara aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Liberiya tun daga shekara ta 2003 a karkashin bukatar kwamitin tsaro na MDD mai doka ta 1509.

Wani rukunin zai tashi zuwa Liberiyan a ranar 17 ga watan nan. Wanda gaba daya rukunin biyu suka kunshi ma'aikata 508 a ciki akwai sojojin bangaren injiniya 275, bangaren sufuri 190 da kuma bangaren kiwon lafiya 43.

Aikin su ya hada da samar da ababen more rayuwa kamar yin hanyoyi da gadoji, gyara a gidajen zama da kuma filin saukan jiragen sama sannan da daidaita ababen samar da ruwan sha da wutan lantarki.

Rukunin har ila yau suna da alhakin jigilar ma'aikata da kayayyakin aiki, samar da ayyukan jinya, bada kariya daga cututtuka da ake saurin dauka da kuma bada kariya tare da magance barkewar annoba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China