in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka 'yan tsagera 25 a tsakiyar Somaliya
2015-08-20 09:14:16 cri

Rahotanni daga Mogadishu, babban birnin kasar Somalaiya sun tabbatar da cewar, sojojin gwamnati sun hallaka 'yan tsagera 25 a cikin kwanaki biyu a wassu kauyuka dake yankin Hiran a tsakiyar kasar.

Wani babban jami'in soji Mohammed Omar ya shaida wa manema labarai cewa, sojojin tare da hadin gwiwwar sojojin kasar Habasha a lokacin karawansu da 'yan tsageran sun samu nasarar hallaka a kalla 25 na 'yan kungiyar Al-Shabaab, galibinsu kuma an hallaka su ne a kauyen Luq Jelow dake yankin na Hiran.

Jamai'in sojin ya tabbatar da cewar, za su ci gaba da aiwatar da ayyukansu har sai sun kwato dukkannin kauyukan da 'yan kungiyar suka kwace, sannan ya musanta zargin cewa, an kashe wassu sojojin daga bangarensu.

Al-Shabaab ita kuma a nata bangaren ta ce, ta yi wa sojojin barna, ta kashe su da dama, abin da jami'in sojin ya karyata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China