Zabukan 'yan majalisun dokokin kasar Masar da aka jima ana jira za su fara a ranar 18 ga watan Oktoba, in ji shugaban hukumar zaben kasar a ranar Lahadi a yayin wani taron manema labarai. Zabukan za su gudana zuwa mataki na biyu a gundumomin kasar 27.
A matakin farko, zabukan za su gudana a gundumomi 14 a ranakun 18 da 19 ga watan Oktoba, sannan gundumomi 13 da suka rage za su gudanar da zabuka a ranakun 22 da 23 ga watan Nuwamba, in ji alkali Ayman Abbas, shugaban babbar hukumar dake kula da aikin shirya zabuka. Kuma zabuka a kasashen waje kuma za su fara a jajibirin kowane mataki.
Hukumar za ta fara karbar takardun 'yan takara daga ranar 1 ga watan Satumba kuma za ta ci gaba har tsawon kwanaki goma sha biyu, in ji mista Abbas. (Maman Ada)