Wasu alkaluma da hukumar dake nazarin harkokin kasuwanci tsakanin bankunan duniya dake kasar Belgium wato Society for Worldwide Interbank Financial Telecommunication ta fitar a alhamis dinnan ya nuna cewar hannayen yari na kudin Yuan yayi matukar habaka lamarin da ya ba kasar Sin damar zama babbar abokiyar huldar kasuwanci ga kasar Afrika ta kudu.
A cewar wani babban jami'i mai sharhi a hukumar dake lura da al'amurran kasuwanci ta kasar Afrika ta kudu Thomas Therry, yace kasar ta tanadi wani tsari na musamman don duba yadda ake ta'ammali da kudaden Yuan bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar huldar kasuwanci tsakanin manyan bankunan kasashen biyu a watan Yuli.
Shi ma Mista Ian de Vleeschawer, wani mai sharhi kan al'amurran kudade na babban bankin kasar Afrika ta kudu cewa yayi, idan har ya kasance aka yi amfani da kudaden Yuan kadai wajen duk wata hada hadar kasuwanci tsakainin kasashen biyu to babu abinda hakan zai haifar sai bunkasa cigaban kasuwancin da samar da yanayi mai tsabta a harkar kasuwanci a tsakanin kasashen. (Ahmad Fagam)