150727-kande.m4a
|
"Yanzu muna iya tuntubar juna ta wayar salula da kuma kafofin sada zumunta na Wechat, amma a shekaru 45 da suka gabata lokacin da muke aiki a Afirka, babu wadannan hanyoyin sadarwa, sai dai ta hanyar wasikun da mu ke samu daga iyalan mu sau daya a ko wane wata. Don haka dukkanmu injiniyoyi muna Alla-Alla mu samu wasiku daga iyalanmu."
Ko da yake kusan yanzu an wuce rabin karni, amma yayin da Lu Datong mai shekaru 80 da haihuwa ya tuna da abubuwan da suka faru a lokacin da yake aikin shimfida layin dogo a tsakanin kasashen Tanzania da Zambia, labaran da ya ke bayarwa sun burge mutane sosai. Wannan injiniya da ya kwashe kusan kashi biyu cikin kashi uku na tsawon rayuwarsa yana wannan aiki na kula da hanyar dogon, yana daya daga cikin injiniyoyi Sinawa fiye da dubu 50 da suka ba da taimako wajen gudanar da wannan aiki.
Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 45 da kaddamar da aikin shimfida hanyar dogo a tsakanin kasashen Tanzania da Zambia, baya ga cikon shekaru 40 da fara zirga-zirga a kan hanyar, inda aka fid da wani sabon littafi na waiwaiye a Alhamis din da ya wuce a birnin Beijing, game da ginin hanyoyin jiragen kasa wadanda suka hada kasashen Tanzania da Zambia, hanyoyin da suka kafa tarihi game da raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.
Cikin littafin, an nuna cewa, a shekarun 1970, kasar Sin ta tallafa wa Afirka wajen shimfida hanyar dogo a tsakanin kasashen Tanzania da Zambia, ko da yake tana fama da mawuyacin hali ta fuskar tattalin arziki. Bisa hadin gwiwa a tsakanin injiniyoyi Sinawa fiye da dubu 50 da jama'ar kasashen Afirka, an cimma nasarar ginin wata muhimmiyar hanyar dogo mai tsayin kilomita 1860.5, wadda ta hada gabashin Afirka da kuma kudanci da kuma tsakiyar nahiyar waje guda. A yayin aikin, kwararrun ma'aikata Sinawa 65 ne suka sadaukar da rayukansu. Kasancewar wannan hanyar dogo ta yi babban tasiri wajen kawar da tsarin nuna wariyar launin fata, gami da gaggauta samun 'yancin kan kabilu, don haka 'yan Afirka su kan kira ta da sunan "hanyar 'yanci kai da sada zumunta".
Sakamakon ingancin hanyar, ya sa MDD a baya ta kira ta da sunan "hanyar dogo mafi nagarta a Afirka" bayan binciken da ta gudanar. A shekarar 1998 kasar Tanzania ta yi fama da wani bala'in ambaliyar ruwa mai matukar muni, inda wasu hanyoyin dogo suka rushe, amma wannan bai shafi hanyar dogo da ke tsakanin kasashen Tanzania da Zambia ba ko kadan. Sai dai sakamakon canje-canjen da aka samu a harkokin zirga-zirga a kasar Tanzania, yanzu wannan hanyar dogo na fuskantar matsalar gudanarwa. Game da wannan, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa,
"Muna da aniya da kuma imanin cewa, za mu iya samo hanyar warware wannan matsala ta hanyar hada kai tare da kasashen Tanzania da Zambia, a kokarin sake zuba sabon jini ga wannan hanyar dogo. Matakin da zai sa kaimi ga wannan tsohuwar 'hanyar 'yancin kai da zumunta' don ta ci gaba da ba da tallafi wajen farfadowar nahiyar Afirka, har ma ta zama wata hanyar bunkasuwa da wadata a zamanin yanzu."
A nasa bangare, jakadan kasar Tanzania a kasar Sin Abdulrahaman A. Shimbo, ya ce, wannan tsohuwar hanyar dogo za ta samar da sabon zarafi ga Sin da Tanzania da kuma Zambia. Yana mai cewa,
"Lokaci ya yi da za a gyara wannan hanyar dogo da aka yi amfani da ita har na tsawon shekaru 40. Bugu da kari, akwai bukatar a kyautata muhimman ayyukan more rayuwa da ke da nasaba da hanyar dogon. Haka zakila, za mu kyautata kwarewar aiki wajen gudanar da ayyukan zirga-zirga, a kokarin tabbatar da ganin jama'a sun ci moriyarsu."
A sa'i daya, Mr. Shimbo yana ganin cewa, a sabon zamanin da ake ciki, hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka na da kyakkyawar makoma. Idan aka dauki hanyar dogo da ke tsakanin kasashen Tanzania da Zambia a matsayin babbar nasarar da aka samu a da, to ana sa ran ganin manyan nasarorin da za a samu nan gaba. Rahotanni na cewa, yanzu kasar Sin na shirin sa hannu kan wasu ayyukan gina hanyoyin dogo a nahiyar Afirka, ciki har da hanyar dogo da ke tsakanin Mombasa zuwa Nairobi na Kenya, da hanyar dogo da ta hada Addis Ababa na Habasha da kasar Djibouti, gami da hanyar dogo mai tsayin kilomita 1400 da ke bakin teku na Najeriya. Duk wadannan sun sheda cewa, yanzu hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka na bude wani sabon babi na inganta dangantakar da ke tsakanin sassan biyu.(Kande Gao)