in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta fannin kiyaye muhalli ya zama abin koyo
2014-07-23 17:33:46 cri

A ranar 22 ga wata ne, aka gudanar da taron manema labarai a hedkwatar hukumar kula da harkokin kiyaye muhalli ta MDD(UNEP) da ke Nairobi, inda aka bayyana nasarorin da aka samu a shirin hadin gwiwar Sin da Afirka na kiyaye muhalli a mataki na biyu.

Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin da hukumar UNEP ne suka kaddamar da wannan shiri na hadin gwiwar Sin da Afirka da ya shafi aikin kiyaye muhalli a shekarar 2008 da nufin inganta kwarewar kasashen Afirka wajen tinkarar sauye-sauyen yanayi ta hanyar yin musayar fasahohi da bayanai a tsakanin masana na kasashen Sin da Afirka. A shekarar 2011 kuma, aka fara gudanar da shirin a mataki na biyu, inda wasu sassan kimiyya na kasar Sin 14 suka fara samar da taimako ga wasu kasashe 16 na Afirka da ke yankin kogin Nilu da tabkin Tanganyika da hamadar Sahara, taimakon da ya shafi adana ruwa da hasashen bala'in fari da bunkasa aikin gona tare da yin tsimin ruwa da hana kwararowar hamada da sauransu. A ganin Mr.Chen Linhao, mataimakin shugaban sashen kula da hadin gwiwa da kasashen waje na ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin, an cimma nasarori masu armashi cikin shekaru uku da aka gudanar da shirin a mataki na biyu, ya ce, "Tawagar kasar Sin da ta Afirka sun kulla huldar abokantaka sosai, bisa goyon bayan hukumar UNEP, an yada fasahohin kasar Sin a Afirka, inda aka samu nasara a fannonin aikin gona tare da yin tsimin ruwa da binciken ingancin ruwa da adana shi da bunkasa aikin gona a yankin da ke fama da karancin ruwa da sauransu, shirin ya kuma jawo hankalin hukumar kiyaye muhalli ta MDD da ma kasashe daban daban, kasashen Afirka ma sun yi maraba da shi, kuma suna fatan za a ci gaba da aiwatar da shirin a mataki na gaba."

Jami'ar Lanzhou ta kasar Sin ma ta sa hannu cikin shirin musamman a bangaren nazarin fasahar noma a yankin da ke fama da karancin ruwa. Xiong Youcai, shehun malami da ke kula da wannan nazarin ya ce, bisa ga gwajin da suka yi cikin shekaru uku da suka wuce a wasu yankuna da ke fama da karancin ruwa a Kenya, fasaharsu na iya kara yawan masara da alkama da ake samarwa da yawa, ya ce, "Idan aka yada wannan fasahar noma a wuraren da ke fama da karancin ruwa a Kenya, hakika za a samu manyan sauye-sauye a bangaren yawan hatsin da ake iya samarwa. Bisa nazarin da muka yi, mun gano cewa, a kashi daya daga ciki uku na filin kasar ta Kenya, za a iya samar da isassun abinci da ke iya ciyar da al'ummar kasar baki daya. In kuma an yada fasahar a fadin kasar baki daya, muna sa ran ganin kasar za ta zama kasar da ke iya fitar da hatsi zuwa ketare a maimakon kasar da ke fama da yunwa."

Dakta Mohamed Abdel-Monem shugaban tawagar kula da muhalli a ofishin hukumar UNEP da ke yankin Afirka ya ce, shirin na hadin gwiwar Sin da Afirka ta fannin kiyaye muhalli ya zama abin misali ga kasashe masu tasowa, ya ce, "Za a kara yada kwarewa da fasahohi masu inganci a mataki na gaba, tare da yin musayar bayanai a fannin kimiyya da kwarewa, hakan ba kawai zai taimaka wa shugabannin kasashen Afirka a yayin da suke fuskantar matsalar kiyaye muhalli, haka kuma zai taimaka wajen warware matsalar." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China