Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Koriya ta Kudu ya bayar, an ce, wani ma'aikacin jinya da ya kamu da cutar kuma ake kula da shi a asibitin Samsung ya yi fama da zazzabi a ranar 2 ga wata, sannan a ranar 10 ga wata, aka fara ware shi.
Wannan ma'aikaci dai ya taba duba lafiyar wasu darurruwan mutane, abin da ke nuna cewa, ya taba mu'amula da wadannan mutane kai tsaye, ko kuma ta wata hanyar. Bisa labarin da aka bayar, an ce, an dauki wannan ma'aikaci ne daga wani asibiti zuwa asibitin Samsung dake Soeul, don haka ba a san irin matakan kandagarki da aka dauka kan ma'aikatan jinyarsa ba, kuma kusan mako guda ke nan ba a killace su ba, don haka ake ganin asibitin ya yi babban kuskure wajen daukar matakan hana yaduwar cutar.(Bako)