Kasar Iran da sauran kasashe 6 a ranar Talatan nan suka fara wani sabon zagaye na tattaunawa a kan batun nukiliyar a kokarin da suke na cimma wa'adin karshe a ranar 30 ga watan Yuni mai kamawa.
Tehran da P5 da karin kasa 1, wato Birtaniya, Sin, Faransa, Rasha da kuma Amurka, sannan da Jamus sun doshi cikakkiyar yarjejeniyar a kan tsarin da aka cimma a Switzerland ranar 2 ga watan jiya na Afrilu, wanda ake fatan kawo karshen ja in jan da ake yi yau shekaru 10.
Abbas Araghchi, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana fatan shi a kan wannan tattaunawar, yana mai cewa, yana da imani, a wannan karon za'a cimma matsaya a daidai wa'adin da aka tsai da.
Wannan yarjejeniya, an yi ta ne da nufin tare da hanyoyin sarrafa nukiliyar ta kasar Iran, a madadin hakan, a samar da saukin rage takunkumin tattalin arziki da aka kakaba mata.
Kasashen yammaci dai sun dade suna zargin ainihin manufar kasar Iran game da shirin nukiliyarta, suna mai cewa, tana shirin aiwatar da makaman nukiliya ne ta fakewa da shirin ci gaban al'umma, ita kuma Iran ta karyata wannan zargin. (Fatimah)