Babban masallacin Dongguan da ke gabashin birnin Xining na lardin Qinghai, yana kuma daya daga cikin manyan masallatai hudu da ke arewa maso yammacin kasar Sin, sa'an nan kuma ya kasance cibiyar cudanyar al'adun musulunci a birnin Xining. Fadin masallacin ya zarce murabba'in mita 18000, kana salon gine-ginensa sun hada da na kasar Sin, da na Turai, da na kasashen Larabawa, gami da na yankin Tibet, matakin da ya shaida cudanyar al'adun kabilu daban daban.