in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lionel Andres Messi ya zama na farko a cikin nagartattun 'yan wasan kwallon kafa 100 na kasa da kasa a shekarar 2012
2012-12-07 18:27:49 cri
Kwanan baya, shahararriyar mujullar wasan kwallon kafa ta kasar Birtaniya wato mujjalar 442 ta zabi shahararrun 'yan wasan kwallon kafa 100 na kasa da kasa a shekarar 2012, inda Lionel Andres Messi na kasar Argentina, wanda ke wasa a kulob din Barcelona na kasar Spain ya zama na farko.

An zaba da kuma tsara wannan jerin sunayen 'yan wasan kwallon kafa masu gwaninta ne bisa yadda suka taka leda a gasanni daban daban a shekarar 2012. Lionel Andrés Messi da Cristiano Ronaldo da Andrés Iniesta sun maye gurabe uku na farko a cikin wannan jerin sunaye, wadanda kuma suke takara da juna domin samun lambar yabo da hukumar kwallon kafa ta kasa da kasa FIFA za ta bai wa dan wasan kwallon kafa mafi nagarta a duniya a shekarar bana. Sa'an nan kuma, Falcao Garcia da Robin van Persie sun zama na 4 da 5. Dan wasan Fernando Torres na kasar Spain, wanda ke wasa a kulob din Chelsea na kasar Birtaniya ya zo na 100. Haka zakila dan wasa Shinji Kagawa na kasar Japan shi ne dan wasan kwallon kafa daya kacal na nahiyar Asiya a cikin jerin sunayen.

Jerin sunayen ya kuma jawo takkadama domin ba a ambaci wasu shahararrun 'yan wasa cikin jerin sunayen ba, kamar Kaká da Marek Cech da Didier Drogba, wanda ke wasa a kasar Sin.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China