Dama akwai yarjejeniyoyin dangantaka tsakanin bangarorin biyu, kamar yadda akwai yarjejeniyoyi tsakanin FIFA da sauran nahiyoyi, amma a wannan karon an kebe wasu muhimman bangarori, musammun ma wajen fasaha da horo kamar horar da kocina, samar da takardun izini, bunkasa aikin alkalan wasa, wasan kwallon kafa daga tushe, kananan yara, samari da 'yan mata, samar da takardun izini ga kungiyoyin wasa, da sauran abubuwa daban daban da suka jibanci wasan kwallon kafa, haka ma da bunkasa aikin likitanci a fannin wasannin motsa jiki.
A cikin wannan dangantaka tasu, FIFA da CAF na fatan hada karfi da karfe da kuma karfafa dangantakarsu tsakanin tsare tsare da ayyukan bunkasa harkokinsu daban daban ta yadda za'a samar da moriya da kuma samarwa kungiyoyin Afrika hanyoyin sa suka dace da su.
Shugaban kungiyar FIFA, Joseph Blatter dake bayyana muhimmancin dangantakar ya nuna cewa a wani lokaci yana da kyau a rika rattaba hannu kan takardu, ko da ana tsammanin babu bukata, tare da bayyana jin dadinsa kan dangantakar dake tsakanin FIFA da CAF da kuma tsakaninsa da shugaba Hayatou. (Maman Ada)