in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana fatan kasar Amurka za ta rika sharhin da ya dace kan sabanin game da mallakar yankuna
2015-05-22 10:59:21 cri

A game da sharhin da kasar Amurka ta fitar kan batun lalacewar yanayin da ake ciki a sakamakon gina tsibirai a tekun kudanci da kasar Sin ta yi, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Hong Lei ya furta a jiya Alhamis cewa, sharhin na kasar Amurka ba gaskiya ba, yana fatan kasar Amurka ba za ta rika ba da irin wannan sharhi ba, kuma za ta kara taka kyakkyawar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Kazalika, Hong Lei ya ce, kasar Sin ta gina tsibiran ne a cikin yankin da take da iko, kuma ta yi haka ne domin ba da hidimomi ga ayyukan ceton mutane da rigakafin bala'u da tabbatar da tsaron jiragen ruwa a teku, ta yadda kasar Sin za ta sauke nauyin dake bisa wuyanta yadda ya kamata, kuma hakan zai kawo moriya ga kasashen duniya.

Ya kuma ce, abubuwan da kasar Amurka ta ke zato ba haka suke ba a zahiri, snnan ba ma kawai ba za su taimaka wajen kawar da sabanin da ke tsakanimsu ba, hatta ma za su kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar, kuma za su ba da kwarin gwiwa ga wasu kasashe wajen daukar matakan tsokana. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China