in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da Afirka a fannin kiwon lafiya bayan an samu nasarar kawar da cutar Ebola
2015-05-20 16:13:37 cri

Direktar hukumar kiwon lafiya da kayyade iyali ta Sin Madam Li Bin dake halartar taron kiwon lafiya na duniya karo na 68 a birnin Geneva ta bayyana wa 'yan jarida a jiya Talata cewa, kasashen yammacin Afirka uku da suka fi fama da cutar Ebola da sauran kasashen duniya sun nuna yabo ga taimakon da kasar Sin ta baiwa wadannan kasashen yammacin Afirka wajen yaki da cutar Ebola. Ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya bayan cimma nasarar yaki da cutar Ebola, da taimakawa kasashen Afirka wajen inganta karfinsu na tinkarar matsalar kiwon lafiya.

A yayin da aka fito hutu a taron kiwon lafiya na duniya da ake gudanarwa, Madam Li Bin ta bayyanawa 'yan jarida na kasar Sin cewa, bayan barkewar cutar Ebola a kasashen yammacin Afirka a shekarar bara, kasar Sin ta kaddamar da ayyukan yaki da cutar ba tare da bata lokaci ba. Sannan ta dauki matakan hana shigowar cutar cikin kasar da shirya matakan tinkarar matsalar, kana ta taimakawa kasashen Afirka da ke fama da cutar wajen yaki da ita, kuma ta samu nasarori da dama a wannan fanni. Li Bin ta ce,

"Sin ita ce kasa ta farko da ta samar da gudummawa ga kasar Saliyo da sauran kasashen yammacin Afirka da ke fama da cutar Ebola, ya zuwa yanzu ta samar da gudummawar kayayyaki da kudade da darajarsu ta kai dala miliyan 120."

Li Bin ta bayyana cewa, tuni akwai rukunonin likitocin kasar Sin dake kasashen yammacin Afirka uku da ke fama da cutar Ebola. Bayan barkewar cutar Ebola, likitocin sun tsaya a kasashen inda suka ci gaba da gudanar da ayyukansu, baya ga haka kuma, Sin ta kara tura likitoci zuwa kasashen uku, kuma adadin likitocin Sin da suka taimakawa kasashen yammacin Afirka wajen yaki da cutar ya kai fiye da 1200 gaba daya. Kana kasar Sin ta fara gudanar da bincike tare da ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar a kasashe 3 masu fama da cutar Ebola a Afirka, da kuma horar da likitocin kasashen uku kimanin dubu 13. Hakazalika kuma kasar Sin ta nuna goyon baya tare da shiga tsarin hadin gwiwar kasa da kasa da MDD da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO suka bullo da shi, inda ta tura masana kiwon lafiya don su shiga tawagar musamman ta MDD da tawagar hukumar WHO dake kasashen Afirka. Wannan shi ne aikin taimakawa kasashen waje a fannin kiwon lafiya mafi girma da Sin ta gudanar tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, kuma kasashen duniya sun yaba wa kasar Sin kan wannan aiki. Li Bin ta bayyana cewa,  

"Gwamnatin Sin tana goyon bayan matakin hukumar lafiya ta duniya WHO na bullo da wani tsarin tinkarar matsalar kiwon lafiya a duniya, da rukunin tinkarar matsalar, da kuma asusun da ake shirin kafawa a wannan fanni. Sin za ta yi kokari tare da kasashen duniya da hukumomin duniya wajen ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya bisa bukatar kasashen Afirka, amincewar Afirka da kuma shigar Afirka cikin wannan aiki, da inganta karfin Afirka na tinkarar duk wata irin matsalar kiwon lafiya da za ta kunno kai."

Game da matakan da Sin ta dauka na magance shigar cutar Ebola cikin kasar, Li Bin ta bayyana cewa, kasar Sin ta cimma burin magance cutar Ebola, ya zuwa yanzu ba a samu rahoton wanda ya kamu da cutar ko ake zaton wani ya kamu da cutar ba, kana likitoci da Sin ta tura da Sinawa dake kasashen da ke fama da cutar dukkansu ba su kamu da cutar ba. Li Bin ta bayyana cewa,

"Bayan barkewar cutar SARS a kasar Sin a shekaru kimanin 10 da suka gabata, kasar Sin ta inganta tsarinta na kiwon lafiya da tinkarar matsalolin kiwon lafiya da su kan kunno kai ba zato ba tsammani. Yanzu karfin Sin a wannan fanni ya kai ma'aunin kiwon lafiya na kasa da kasa. Musamman yayin da muke yin kokarin yaki da cutar Ebola a wannan karo, Sin ta kara samun fasahohi, kamar kara kyautata tsarin tinkarar matsalar kiwon lafiya, da kuma gaggauta yin kirkire-kirkire a fannin nazarin maganganu."(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China