in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin UNHRC ya tantance yanayin hakkin dan Adam na Amurka
2015-05-12 11:07:58 cri

A jiya Litinin, rukunin kwamitin hakkin dan Adam na MDD UNHRC ya tantance yanayin hakkin dan Adam na kasar Amurka, inda wakilan kasashe 122 suka yi jawabi a gun taron, domin ba da shawara kan halin hakkin dan Adam na kasar Amurka.

Batutuwan da wakilan suka ambata game da hakkin dan Adam su ne tsaurara gudanar da shari'u da nuna bambancin kabilu da addinai da kuma jinsi, da kafa gidan kurkuku na Guantanamo da dai sauransu.

Wakilin kasar Sin ya dora muhimmanci sosai kan batutuwan hakkin dan Adam na kasar Amurka, kuma ya ba da shawarwari kan batutuwan tsaurara yanke hukunci kan 'yan asalin Afrika da sauran kananan kabilu, da azabtarwa ba bisa doka ba, da tona asirin jama'ar kasar, da girmama iko da moriyar mutanen kananan kabilu dake zama a kasar, da kuma amince da yarjejeniyar ikon yara tun da wuri.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China