in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi zanga-zanga a birnin Johannesburg don nuna adawa da kyamar baki a kasar Afrika ta kudu
2015-04-24 16:36:13 cri

A jiya Alhamis 23 ga wata a birnin Johannesburg dake kasar Afirka ta Kudu, an yi zanga-zanga don nuna adawa da kyamar baki a kasar, inda jama'ar kasar da 'yan kasashen waje dake kasar fiye da dubu 30 suka bazama kan tituna don nuna adawa ga tashe-tashen hankulan nuna kyamar baki da aka yi a biranen Durban da Johannesburg a kwanakin baya.

A ranar Litinin 23 ga wata, gwamnan jihar Gauteng da ke kasar Afirka ta Kudu David Makhura da magajin birnin Johannesburg Parks Tau sun jagoranci masu zanga-zanga fiye da dubu 30, inda suka ratsa wasu titunan dake tsakiyar birnin Johannesburg, kana suka isa dandalin Mary Fitzgerald. A kan hanyarsu, masu zanga-zanga sun daga alluna dake dauke da kalmomin "nuna adawa da kyamar baki da dakatar da tashe-tashen hankula" tare da yin kiran koke:

"Hada kai da nuna adawa ga nuna kyamar baki!"

Tsohon ministan ma'aikatar leken asiri na kasar Afirka ta Kudu, kuma masani kan zamantakewar al'ummar kasar Ronnie Kasrils ya yi jawabi yayin a wurin zanga-zangar, inda ya nuna adawa ga kyamar baki daga nahiyar Afirka da Asiya da sauran kasashen duniya da suke rayuwa a kasar Afirka ta Kudu.

A watan da ya gabata, tashe-tashen hankulan nuna kyamar baki a kasar Afirka ta Kudu sun haddasa mutuwar mutane a kalla 7, yayin da 'yan kasashen waje fiye da dubu daya suka rasa gidajensu, lamarin da ya tilasta musu zama a sansanin 'yan gudun hijira. Don nuna damu game da ci gaba da samun tashe-tashen hankulan nuna kyamar baki, jama'a daga kasashen Zimbabwe da Malawi fiye da dari daya sun fice daga kasar Afirka ta Kudu bisa kariyar gwamnatocin kasashensu. Kana wasu sauran 'yan kasashen Afirka dake kasar Afirka ta Kudu suna duba yiwuwar ficewa daga kasar, sakamakon tsoron a kore su ko a fadawa cikin hare-hare da wasu 'yan Afirka ta kudu ke kaiwa 'yan kasashen waje da ke kasar suke yi.

A cikin tawagar masu zanga-zangar, wasu mutane sun daga hoton Nalson Mandela don tunawa da tarihi wajen yin kashedi. Wani dan kasar Nijeriya mai suna Jason ya bayyana cewa.

"Mun taba nuna kyamar wariyar launin fata da ra'ayin mulkin mallaka, yanzu ya kamata mu yi amfani da irin wannan hanya wajen nuna adawa da kyamar baki."

Tashe-tashen hankulan nuna kyamar baki da aka samu a kasar Afirka ta Kudu sun haddasa korar 'yan kasar Afirka ta Kudu a wasu kasashen Afirka da suka mayar da martani. Kamfanin hakar ma'adinai na Ireland da kamfanin Sasol dake kasar Mozambique sun kori ma'aikata daga kasar Afirka ta Kudu a kwanakin baya. Kana an yi zanga-zanga da nuna adawa a wasu ofishin jakadancin kasar Afirka ta Kudu dake wasu kasashen Afirka. Fada Paul ya yi jawabi a yayin zanga-zangar, inda ya yi kira da a dakatar da nuna kyamar baki da tada rikici a tsakanin al'ummomi daban daban. Ya ce,

"Ba za a ci gaba da nuna adawa ga 'yan kasar Afirka ta Kudu a wasu kasashen Afirka ba. Kamata ya yi a nemi wata hanya don nuna daidaici ga dukkan mutane."

Bayan da aka samun tashe-tashen hankulan nuna kyamar baki a kasar Afirka ta Kudu, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa, akwai bukatar tattaunawa da kyautata manufofin 'yan cin rani na kasar don kyautata dangantakar dake tsakanin jama'ar kasar Afirka ta Kudu da 'yan kasashen waje. Ministan harkokin cikin gida na kasar ya bayyana cewa, watakila za a gabatar da wata takarda da ke bayani kan dokokin da suka shafi 'yan cin rani a shekarar 2016, inda za a yi gyaran fuska ga dokokin da suka shafi 'yan cin rani a kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China