Yan tawaye a yankin Darfur da ake gwabza fada sun yi ikirarin cewa, sun yi galaba a fadan da suke da dakarun gwamnatin a yankin Kutum da ke arewacin Darfur, lamarin da sojojin na Sudan suka karyata.
Cikin wata sanarwa da 'yan tawaye da kuma sojojin kwatar 'yancin Sudan (SLA) suka fitar, sun bayyana cewa, sun yi arangama da dakarun gwamnati a yankin Kutum, kilomita 70 arewa da El Fasher, babban birnin jihar Darfur, inda aka halaka sojojin gwamnati kimanin 60, ciki har da wani kwamanda da mataimakinsa, baya ga motocin soja guda 10 da suka kwace, sannan suka kona wasu guda 9.
Sai dai kakakin sojojin gwamnatin Sudan Al-Sawarmy Khalid Sa'ad ya karyata ikirarin 'yan tawayen, yana mai cewa, su ne suka samu galaba a kan 'yan tawayen. Ya kuma ce, hakika an kashe tare da jikkata wasu sojoji, amma bai bayyana adadinsu ba.
Sojojin Sudan sun bayyana cewa, ko da a watan da ya gabata ma sun murkushe wani hari da mayakan 'yan tawayen suka yi niyar kaiwa a kudancin Darfur, inda suka zargi Sudan ta Kudu ta taimakawa 'yan tawayen.
A baya-bayan nan fada tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da 'yan tawayen Darfur ya kara kamari dai-dai lokacin zaben shugaban kasar Sudan wanda shugaba mai ci Omar al-Bashir ya sake lashewa.(Ibrahim)