in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
COMESA ta tura masu sa ido ga zabe a Sudan
2015-04-09 10:01:06 cri

Kungiyar hadin gwiwar kasuwanci ta kudunci da gabashin Afrika (COMESA) ta tura wata tawagar masu sa ido domin sanya ido kan zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki na ranar 13 ga watan Afrilu mai zuwa a kasar Sudan, in ji kungiyar COMESA a ranar Laraba.

A cikin wata sanarwar sakatariyar COMESA dake birnin Lusaka, hedkwatar kasar Zambiya, shugaban tawagar Immacule Nahayo ya tabbatar da cewa, tura wannan tawaga ta masu sa ido ta samu goron gayyata ne daga gwamnatin kasar Sudan.

Tawagar masu sa ido, da ake sa ran ta isa tun ranar Laraba a kasar Sudan, ta hada da manyan jami'an gwamnatocin kasashe goma, mambobin kungiyar COMESA, in ji wannan sanarwar.

Tawagar kuma za ta tsaya a Sudan har zuwa ranar 16 ga watan Afrilu, za ta sanya ido ga matakin karshe na ayyukan kusa da zabe, da zaben kansa, kidayar kuri'u da bayar da sakamakon zabe.

Shugaban tawagar ya kuma bayyana cewa, tawagarsa za ta tattauna tare da masu ruwa da tsaki kan zabukan kasar, kungiyoyin fararen hula, kafofin watsa labarai da manyan hukumomin dake kula da shirya zabe, tare kuma da yin shawarwari tare da jakadun kasashen waje da sauran tawagogin sa ido ga zaben. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China