in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya kara wa'adin aikin UNAMID a Darfur
2014-08-28 10:59:26 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya kara wa'adin aiki na watanni 10, ga rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da AU wato UNAMID, wacce ke Darfur a kasar Sudan.

Kasashe 15, dake cikin kwamitin tsaron na MDD sun amince da karin lokacin da aka baiwa sojojin nan zuwa 30 ga watan Yuni na shekarar 2015, a cikin wani kuduri wanda suka amince da shi.

Kwamitin tsaron ya bukaci rundunar kiyaye zaman lafiyar ta UNAMID, da ta mai da hankali musamman wajen cika sharuddan umurnin da aka ba ta tun farko, wanda ya hada da bayar da kariya ga farar hula, da kuma tabbatar da tsaro na kayayyakin agaji da ake shigowa da su kasar ta Sudan.

Hakazalika kwamitin tsaron ya bukaci rundunar kiyaye zaman lafiya ta UNAMID, da ta aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyanta na kare fararen hula, da kuma yin aiki tare da gwamnatin Sudan, da kuma tabbatar da yancin walwalar jama'a da tsaron lafiyar ma'aikatan rundunar ta UNAMID da ma'aikatan agaji.

Kudurin kwamitin tsaron na MDD ya bukaci dukannin kungiyoyin dake fada da juna a Darfur, wadanda suka kunshi kungiyoyi masu dauke da makamai, wadanda ba su rattaba hannunsu a kan yarjejeniya ba, da su tsagaita wuta nan take, ba tare da bata wani lokaci ba, domin a samar da dawwamammen zaman lafiya mai dorewa a yankin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China