in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara tabbatar da ikon mallakar ilmi
2015-04-27 10:39:22 cri
Ranar 26 ga watan Afrilu rane ce ta ikon mallakar ilmi na duniya. Shugaban hukumar kula da ikon mallakar ilmi ta kasar Sin Shen Changyu ya bayyana cewa, ikon mallakar ilmi tushe ne na tabbatar da yin kirkire-kirkire, kana shi ne gada dake hada fasahohi da karfin samar da kayayyaki a halin yanzu.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan bukatar mallakar fasaha a shekarar 2014 ya kai dubu 928, wanda ya karu da kashi 12.5 cikin dari bisa na shekarar 2013. Kuma yawan mallakar fasaha da aka amince a shekarar 2014 ya kai dubu 233, wanda ya karu da kashi 12.3 cikin dari bisa na shekarar 2013.

Shen Changyu ya bayyana cewa, ikon mallakar ilmi ya warware matsalar dake kasancewa yayin da ake canja fasahohi zuwa karfin samar da kayayyaki. A mataki na gaba, hukumar kula da ikon mallakar ilmi ta kasar Sin za ta kara kirkiro da yin amfani da tabbatar dakyautata ayyukan da ke da nasaba da ikon mallakar ilmi, don sa kaimi gakara karfafa ma dukkan al'umma da su gwiwa na yin kirkire-kirkire da nuna goyon baya ga bunkasuwar aikin kirkire-kirkire. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China