in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara nuna gamsuwa ga aikin kare ikon mallakar ilmi da fasaha a kasar Sin
2015-04-24 15:56:09 cri

A yau ne a nan birnin Beijing aka gabatar da rahoton nazari game da gamsuwar mutane kan aikin kare ikon mallakar ilmi da fasaha na shekarar 2014 gabanin ranar ranar 26 ga wata wato ranar kare ikon mallakar ilmi da fasaha ta duniya.

Rahoton ya ce, an kara nuna gamsuwa da yadda ake gudanar da aikin kare ikon mallakar ilmi da fasaha a kasar cikin shekaru 3 a jere.

Babban sakataren hukumar kare ikon mallakar ilmi da fasaha ta kasar Sin Xiao Luqing ya ce, Tun daga shekarar 2012, a shekaru uku a jere ne kasar Sin ta yi nazari game da ra'ayoyin jama'a kan aikin kare ikon mallakar ilmi da fasaha, inda aka kara nuna gamsuwa kan wannan aiki a ko wace shekara, ko da yake aikin na bukatar kara kyautatuwa.

Sakamakon da aka samu a wannan nazari ya bayyana cewa, sassa daban daban na kasar Sin sun nuna matukar gamsuwa ga hidimomin da aka bayar wajen kare ikon mallakar ilmi da fasaha da yadda aka ilimantar da jama'a game da wannan aiki, kana dokoki da manufofin da aka shata kan wannan aiki sun samu martanin kamar yadda aka yi a lokacin baya .(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China