in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin mota ya kashe mutane goma a Mogadishun Somaliya
2014-10-13 10:55:56 cri

A kalla mutane 10 suka mutu a cikin wani harin motar da aka danawa bom da ya faru a ranar Lahadi a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya. Fashewar bom din ta faru kusa da Oroma Cafe, wani dakin shan kofi dake cike da mutane, da kuma kan hanyar Maka Al Mukarrama tsakanin filin jirgi da fadar shugaban kasar.

Yan sandar wurin suna ganin cewa, an tada bom din ne daga nesa. Sai dai har yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin. A baya, kungiyar kishin islama ta Al-shabaab ta dauki alhakin kai irin wadannan hare-haren a cikin kasar ta Somaliya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China