in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin bam ya halaka mutane 5 a Mogadishu
2014-10-16 09:55:59 cri

A kalla mutane biyar ne suka halaka, kana wasu da dama suka jikkata yayin da wani bam da aka dana a cikin wata mota ya fashe a kusa da wata mashaya a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, harin da ya kasance na biyu cikin mako guda.

Wasu da lamarin ya faru a kan idonsu sun bayyana cewa, motar da aka dana bam din a cikin ta ta tarwatse ne a kusa da mashayar Panorama da ke kusa da babban titin Makka Al Mukarrama, inda ya kashe mutane biyar, ciki har da yara, sannan wasu da dama suka jikkata.

Rahotannin kafofin watsa labarai sun tabbatar da yawan mutanen da suka mutu, sai dai mai yiyuwa adadin zai karu saboda wasu mutanen raunin nasu ya yi tsanani.

Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, amma ana zargin kungiyar mayakan nan ta Al-Shabaab da kai irin wadannan hare-hare a Somaliya.

Harin na wannan karo ya zo ne bayan wani hari makamancin wannan da baya ga wasu fiye da 20 da suka rasa rayukansu, da kuma wasu sama da 30 da suka jikkata, galibinsu fafaren hula. Sai dai kungiyar Al-Shabaab ba ta bayyana cewa ita ce ta kai harin ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China