in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AIIB zai cimma moriyar juna tare da bankunan raya kasashen duniya, a cewar firaminista Li Keqiang
2015-03-24 09:14:39 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban bankin raya nahiyar Asiya Takehiko Nakao a jiya Litinin 23 ga wata a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, a matsayin kasa mai tasowa mafi girma, kasar Sin tana da burin inganta dangantakar dake tsakaninta da bankin raya Asiya, kana tana fatan bankin zai taka muhimmiyar rawa, wajen sa kaimi ga kawar da talauci, da samar da bunkasuwa a yankin Asiya da tekun Pasific.

Haka zalika kuma, Li Keqiang ya yi nuni da cewa, Sin ta yi kira ga kafa AIIB ne domin sa kaimi ga aikin hadin gwiwa, da bunkasa tattalin arziki, da zamantakewar al'umma a yankin. Ya ce AIIB zai bude kofa, da juriya, da yin hadin gwiwa tare da bankunan raya kasashen duniya, domin cimma moriyar juna.

A nasa bangare, Takehiko Nakao ya bayyana cewa, bankin raya Asiya ya jinjinawa bunkasuwar Sin, da nasarorin da ta samu wajen yaki da talauci. A ganinsa fasahohin Sin suna da amfani ga dukkan duniya wajen samun bunkasuwa. Kuma kafuwar AIIB ta dace da bukatun bunkasuwar tattalin arzikin wannan yanki. Kaza lika bankin raya Asiya yana fatan yin hadin gwiwa tare da AIIB. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China