in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta jaddada cewa babu rufa rufa a cewa Kofar bankin zuba jari na AIIB a bude take, in ji kasar Sin
2015-03-23 20:18:18 cri
Kasar Sin ta jaddadad matsayinta na maraba da kasa da kasa su sa hannun kafa gudanar da ayyukan ta a fili da suka hada da gina tare da tafiyar da bankin zuba jarin game da muhimman ababen more rayuwar kasashen Asiya na yankin Asiya (AIIB), in ji kakakin ma';aikatarn harkokin wajen ta.

Kakakin Hong Lei ya bayyana hakan ne ga manema labarai a nan Birnin birnin Beijing lokacin da yake Karin karin haske akan tambayar cewa ko kasar nada aniyar hadin kai da Amurka wadda a baya ta yi kira ga kawayenta da kada su shiga bankin..

Mr Hong yace sauyin matsayi da Amurka keyi ya nuna cewa kudurin da bankin na AIIB ta dauka na samar da ababen more rayuwa a yankin Asia ya samu karbuwa.

A nashi bayanin shi ma Sakatare sakatare janar na ofishin wucin gadi mai kula da bankin AIIBsaka jari game da muhimman ababen more rayuwar kasashen Asiya, wato AIIB ,Ya ya ce Sin tayi tayin kafa wannan bankin ne domin ta cimma burin da yankin ke da shi na samar da ababen more rayuwa.

Gwamnatin Barrack Obama na Amurka ta yi tayin hadin gwiwwa tsakanin bankin na AIIB da sauran hukumomin kudi na duniya kamar su bankin duniya, kamar yadda jaridar wall street journal na Amurkan ta bayyana a jiya lahadi.

A yanzu haka dai bankin nada mambobi 27 da suka nuna sha'awar su na shiga cikin bankin. Haka kuma kasashen Birtaniya, Faransa, Jamus, Italiya, Luxembourg da Switzaerland su ma kwanan nan suka bukaci izni shiga cikin mambobin bankin.

Mr Jin yana sa ran adadin masu bukatar shiga ya karu zuwa 35 nan da karshen shekarar wannan wata da muke ciki lokacin da za'a rufe karban karbar takardun neman izini.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China