Kwamitin ministocin kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA), ya yi maraba da ci gaban tattalin arzikin mai gamsarwa da aka samu a cikin kasashe mambobin kungiyar da ke bayyana cigaban kayayyakin cikin gida da ake sarrafawa wato GDP na wannan kungiya ya kai kashi 6,8 cikin 100 a shekarar 2014 idan aka kwatanta da na shekarar 2013 dake kashi 5,9 cikin 100, duk da rashin karfin farfadowar tattalin arzikin duniya, in ji wata sanarwar da aka fitar a ranar Talata a birnin Cotonou na kasar Benin.
A cewar wannan sanarwa da ta kawo karshen zaman taron kwamitin ministocin UEMOA da aka bude a ranar Litinin a birnin Cotonou, wannan ci gaban zai dore bisa cigaban kuzarin bangarorin noma da na masana'antu, haka ma da ci gaban bangaren gine-gine. (Maman Ada)