Shugaban Nigeriya mai barin gado Goodluck Jonathan a ranar Laraban nan ya ce, ya cika alkawarin da ya yi na tabbatar da zabe cikin adalci da gaskiya a kasar, bayan da ya amince da shan kaye a babban zaben da aka yi a karshen makon nan.
Goodluck Jonathan a cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan rana ya ce, ya cika alkawarin shi kuma ya ba da sarari ga 'yan kasa su aiwatar da 'yancinsu na demokradiya, kuma jam'iyarsa sai dai ta yi murnan haka maimakon bakin ciki.
A wani kokari da ya yi na kwantar da hankalin magoya bayansa, ya bukace su da su bi dokar tsarin mulkin kasar.
Shugaban mai barin gado dai a ranar Talata ya amince da shan kaye inda ya buga wayar ba zata ga abokin hamayyarsa 'dan jam'iyar kuma zababben shugaban kasa APC Muhamadu Buhari don taya shi murnan a kan nasarar da ya yi. (Fatimah)