Bayan da aka kammala jefa kuri'u a ranar Lahadi, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC ta fara kidayar kuri'u a cibiyar taron kasa da kasa ta Abuja.Bisa sakamakon da aka samu, an ce, Muhammadu Buhari ya samu kuri'un da yawansu ya kai kashi 53.95 cikin dari, yayin da Jonathan ya samu kashi 44.96 cikin dari.
Wannan shi ne karo na farko, da jam'iyyar PDP ta fadi babban zabe cikin shekaru 16 da ta kafa gwamnati, wanda ta samu shugabannin kasar da suka hada da Olusegun obasanjo, marigayi Umaru Musa Yar 'Adua da kuma Goodluck Jonathan.(Bako)